Dubun dubatar musulmi masu ibada ne suka gudanar da sallar Juma’a ta biyu na watan Ramadan a harabar masallacin Al-Aqsa, duk da tsauraran matakan da Isra’ila ta dauka na hana Falasdinawa shiga wurin mai tsarki.
Sashen kula da masallacin da ke birnin al-Quds ya ce kimanin masu ibada 80,000 ne suka taru A daidai lokacin da ake fargabar ci gaba da tashin hankalin da gwamnatin Isra’ila ke yi ga mazauna yankin.
Duk da wannan takunkumin, masu ibada sun yi ta tururuwa daga yankuna daban-daban na Yammacin Kogin Jordan don shiga wurin mai tsarki.
Sojojin Isra’ila sun hana matasan Falasdinawa shiga daga Jenin da Tulkarm.
Hamas ta yi Allah wadai da takunkumin Isra’ila a Masallacin Al-Aqsa