Sama da jiragai marasa matuka 160 na makiya Iran ta kakkabo tun soma yakin Amurka da Isra’ila

Hedikwatar rundinar sojojin sama ta iran ta sanar da cewa sama da jiragai marasa matuka 160 ne ta kakkabo tun bayan soma yakin da Amurka
Sama da jiragai marasa matuka 160 na makiya Iran ta kakkabo tun soma yakin Amurka da Isra’ila

Hedikwatar rundinar sojojin sama ta iran ta sanar da cewa sama da jiragai marasa matuka 160 ne ta kakkabo tun bayan soma yakin da Amurka da isra’ila suka kaddamar kan kasar.

Baya ga jiragai marasa matuka da akwai wasu jiragen yaki da kuma makamai masu linzami samfarin cruise da aka kakkabo.

A wata ziyara ga sojojin da kuma dakarun kare juyin juya halin musulinci kwamandan rundinar sojin sama ta iran birigediya janar Alireza Elhami ya bayyana cewa daga cikin jiragan da aka kakkabo har da samfarin MQ-9, da Hermes, and LUCAS da kuma dozin dozin na makamai masu linzami samfarin cruise.

Ya kuma ce sojojinsa sun shirya tsaf wajen tunkarar jiragan yaki da jiragai marasa matuka na makiya.

Ya kara da cewa kakkabo irin wadanan jiragan na zamani na makiya da dakarunsa da na IRGC sukayi sakamako ne na dabaru da kuma sabbin na’urorin da iran ta ke da su na kare hare hare daga sararin samaniya wadanda suke zama kalubale ga sojojin makiya.

Amurka da isra’ila sun kaddamar da yaki kan iran ne ba tare da wani dalili ba a ranar 28 ga watan Fabarairu inda a ranar farkon yakin jagoran juyun juya halin musulinci na iran, Ayatollah sayyid Ali khamenei da kuma wasu manya manyan kwamandojojin sojin kasar da fararen hula da dama suka yi shahada.

A matsayin maida martani iran ta kaddamar da hare-hare kan kan isra’ila da kuma sansanoni soji da cibiyoyin Amurka a wasu kasashen yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted