DRC : An yanke wa Joseph Kabila hukuncin kisa kan cin amanar kasa

Kotun koli ta Soji a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo ta yanke wa tsohon shugaban kasar Joseph Kabila hukuncin kisa bisa samunsa da laifin cin amanar kasa

Kotun koli ta Soji a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo ta yanke wa tsohon shugaban kasar Joseph Kabila hukuncin kisa bisa samunsa da laifin cin amanar kasa da laifukan yaki ciki har da jagorantar kungiyar ‘yan tawayen M23.

An samu Kabila da laifuffuka da dama da suka hada da shiga wani yunkuri na tayar da kayar baya, cin amanar kasa, azabtarwa, da kuma laifukan yaki, a cewar hukuncin da kotu ta yanke a Kinshasa, babban birnin kasar.

An fara shari’ar tasa ne a watan Yuli, bayan da majalisar dattawa ta tsige masa  rigar kariya a watan Mayu, bisa zarginsa da hannu a ta’asar da ‘yan tawayen M23 suka aikata a lardunan gabashin Congo.

Kotun ta ce Mista Kabila “ya gudanar da tarurrukan kiran yaki (a manyan lardunan Goma da Bukavu).

Kabila ya mulki kasar ta Jamhuriyar Demokuradiyyar Congo, daga shekarar 2001 zuwa 2019, amma yana rayuwa ne a Afrika ta Kudu tun daga shekarar 2023.

Amma a farkon wannan shekarar, ya bayyana a gaban jama’a a gabashin Congo tare da bayyana muradinsa na komawa gida don “ba da gudumawar neman mafita” kan rikicin da ake ciki yanzu.

Gabashin Congo ya fuskanci daya daga cikin rikice-rikice mafi dadewa a Afirka.

Tun daga watan Janairu, lamaran tsaro sun tabarbare sosai, inda aka sake samun barkewar fada tsakanin dakarun gwamnati da ‘yan tawayen M23, wadanda suka kwace wasu muhimman yankuna da suka hada da Goma da Bukavu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted