DRC: An Killaci Matafiya A Jirgin Ruwa Bayan Da Ebola Ta Kashe Daya Daga Cikinsu

Mutanen da suke cikin jirgin ruwan a kasar DRC sun kai 200 yayin da wani daga cikinsu ya rasa ransa bisa zargin cewa Ebola ce

kokarin hana yaduwar Ebola

Mutanen da suke cikin jirgin ruwan a kasar DRC sun kai 200 yayin da wani daga cikinsu ya rasa ransa bisa zargin cewa Ebola ce ta kashe shi.

Mahukuntan kiwon lafiya na kasar ta DRC sun killace sauran matafiyan domin gudanar da bincke akan lafiyarsu saboda a dakile cutar da hana yaduwarta a tsakanin mutane.

Shugaban hukumar hada yaduwar cutuka ta Afirka Jean Kaseya ya fada a jiya Alhamis cewa; An killace matafiyan ne har da ma wadanda a Zahiri babu alamun cutar a tre da su, saboda a tabbatar da cewa babu wanda ya kamu da ita.

Cibiyar bincike na ( INRB) tana gudanar da bincike akan mutanen, ba kuma za a bar su,su shiga cikin birnin Kinshasha ba, har sai sakamakon bincike ya fito.

Mutuwar matafiyin akan wannan jirgin ruwan ya sa an sake shiga zullumi akan yaduwar wannan cuta wacce take cin kwan makauniya a kasar DRC da makwabtanta.

Watannin baya kadan an sami bullar wannan cutar a kasar ta DRC da ta ci rayukan mutane, sannan kuma ta bulla a kasar Uganda dake makwabtaka da ita.

Kasa kamar Rwanda ta rufe iyakarta da DRC domin hana shigar cutar cikinta.

Sai dai daga bayan an sami sassauncin tsauraran matakan da aka dauka akan iyaka, da ya bayar da damar ci gaba da zirga-zirgar kasuwanci.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted