Kungiyar M23 da ke dauke da makamai a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango, ta yi watsi da tattaunawar zaman lafiya da gwamnatin kasar, tana mai cewa ba za ta koma tattaunawa ba, sai dai idan hukumomi sun cika sharuddan yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka cimma a baya.
Rikicin da aka gwabza tsakanin dakarun gwamnati da mayakan na M23 a watan Janairu ya kara kamari, yayin da kungiyar mai dauke da makamai ta kwace iko da yankuna masu yawa a yankin gabashin kasar mai arzikin ma’adinai, kafin dukkan bangarorin biyu su cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a tattaunawar da aka yi a Qatar a watan da ya gabata, wanda ke da nufin share fagen samar da zaman lafiya mai dorewa.
Kungiyar ta M23 ta sanar a ranar Litinin cewa tawagarta ba ta koma kasar Qatar ba kamar yadda aka tsara za a ci gaba da tattaunawar zaman lafiya, yayin da kakakin kungiyar Lawrence Kanyuka ya shaidawa wasu kafofin yada labarai cewa matakin da gwamnatin Kongo ta dauka na nuna cewa “ba ta son zaman lafiya”, wanda hakan ke nuna shakku kan makomar shawarwarin.
Kanyuka ya zargi mahukuntan Kongo da karya sharuddan yarjejeniyar tsagaita bude wuta, yana mai cewa dakarun gwamnati sun ci gaba da kai hare-hare kan wuraren da ‘yan tawayen suke, duk da yarjejeniyar da ta tanadi cewa bangarorin biyu su dakatar da yakin, yayin da sojojin DR Congo suka yi watsi da wadannan zarge-zargen, tare da bayyana cewa babu kamshin gasiya a cikinsu.
A gefe guda kuma, Kongo ta zargi dakarun M23 da kai hare-hare a kusan kowace rana a lardin Kivu ta Arewa da Kivu ta Kudu.