Doha: Pakistan da Afghanistan sun amince da tsagaita bude wuta a tsakaninsu

Ma’aikatar harkokin wajen Qatar ta sanar da cewa, kasashen Pakistan da Afghanistan sun amince da tsagaita bude wuta nan take a tattaunawar da ake yi

Ma’aikatar harkokin wajen Qatar ta sanar da cewa, kasashen Pakistan da Afghanistan sun amince da tsagaita bude wuta nan take a tattaunawar da ake yi a Doha babban birnin kasar.

Ma’aikatar ta tabbatar da cewa bangarorin biyu sun amince da tsagaita bude wuta a wani zagayen shawarwarin da kasashen Qatar da Turkiyya suka jagoranta a ranar Asabar.

Ma’aikatar ta kara da cewa kasashen biyu sun kuma amince da da a ci gaba da tattaunawa a cikin kwanaki masu zuwa don tabbatar da dorewar tsagaita bude wuta.

Ministan tsaron Pakistan Khawaja Muhammad Asif ya ce bangarorin biyu za su sake ganawa a ranar 25 ga watan Oktoba a Istanbul domin tattauna batutuwan da suka shafi ci gaban da aka samu game da hakan.

A baya dai bangarorin biyu sun sanar da cewa za su gudanar da tattaunawar zaman lafiya a Doha a kokarin da suke na kawo karshen rikicin da ya barke a kan iyakar Afghanistan da Pakistan a cikin kwanakin nan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments