Firaministar kasar Denmark Mette Frederiksen, wadda a halin yanzu kasarta ke rike da shugabancin kungiyar Tarayyar Turai ta bayyana a wata sanarwa ga manema labarai a jiya Asabar cewa, kasarta na shirin kakabawa Isra’ila takunkumi, sakamakon yakin da take yi a zirin Gaza da yammacin kogin Jordan.
A wata hira da ya yi da Jyllands-Posten, Frederiksen ta ce “Yanzu Netanyahu ya zama matsala shi a kan kansa,” tana mai cewa “gwamnatin Isra’ila ta wuce gona da iri.”
Ta bayyana halin da ake ciki na jin kai a Gaza a matsayin “mummunan bala’i,” tare da sukar shirin Isra’ila na ci gaba da aikin tsugunar da jama’a a Yammacin Kogin Jordan.
Firaministar Denmark ta jaddada cewa kasarta na cikin kasashen da ke neman kara matsin lamba kan Isra’ila, amma har yanzu baki bai zo daya kan wannan batu a tsakanin dukkanin mambobin kungiyar EU ba.
Ta kara da cewa tana son yin amfani da “matsi na siyasa da takunkumi, ko a kan ‘yan share wuri zauna ko ministoci, ko ma a kan gwamnatin Isra’ila baki daya.
Kimanin mako guda da ya gabata ne ministan harkokin wajen Denmark Lars Løkke Rasmussen ya yi kira ga Isra’ila da ta gaggauta janye matakin da ta dauka na mamaye yankin zirin Gaza, yana mai nuna matukar damuwarsa kan halin da ake ciki na jin kai da kuma wahalar da ake fuskanta wajen kai agajin jin kai ga al’ummar Gaza.