Daruruwan Yan Kasar Chadi Sun Fito Zanga-Zangar Kin Samuwar Sojojin Faransa A Kasar

Daruruwan mutanen kasar Chadi sun fito zanga-zangar bukatar gwamnatin kasar Faransa ta fidda sojojinta daga kasar a jiya Jumma’a. Shafin yanar gizo na labarai Afirca

Daruruwan mutanen kasar Chadi sun fito zanga-zangar bukatar gwamnatin kasar Faransa ta fidda sojojinta daga kasar a jiya Jumma’a.

Shafin yanar gizo na labarai Afirca News ya bayyana cewa na gudanar da zanga-zangar ne mako guda da gwamnatin kasar ta kawo karshen yarjeniyar samar da sojojin Faransa a kasar. A birnin Njamena babban birnin kasar masu zanga zangar suna rera taken ‘Chadi namu ne, Faransa fita daga kasarmu’ wasu kuma suna cewa ‘ ba masa son ganin mutumin kasar Faransa ko guda a kasarmu’.

Labarin ya kara da cewa, a makon da ya gabata ne gwamnatin kasar ta Chadi ta bada sanarwan cewa ta kawo karshen yarjeniyar tsaro da kasar Faransa, kuma ba zata sake sabontashi ba saboda tana son wani sabon tsari a harkokin tsaron kasar. Kasar Faransa dai tana da sojoji kumani 1000 guda a kasar ta Chadi, amma ba’a san lokacinda zata dauke su daga kasarba, bayan da aka kawo karshen yarjeniyar tsaro tsakaninta da gwamnatin kasar ta Chadi. Labarin ya kammala da cewa masu zanga-zangar sun je sansanin sojojin kasar ta Chadi a Njemaina suna bayyana ra’ayinsu, a yayinda wasu suka je ofishin jakadancin kasar Chadi a birnin suna bayyana wannan bukatar. Amma gwamnatin ta santa jami’an tsaro masu yawa don kare shi daga duk wanda zai yi kokarin yin abinda bai dace ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments