Dangantaka tsakanin Nijar da Algeria na ci gaba da kara karfi

kasar niger da aljeriya na kara karfafa dangntakar dake tsakaninsu

Ministan Mai da Iskar Gas na Aljeriya, Mohamed Arkab, ya fara ziyarar aiki ta kwanaki biyu a Nijar, wadda ta fara a ranar 21 ga watan da muke ciki.

  A cewar wata sanarwa, ziyarar ta mayar da hankali ne kan duba ayyukan hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu a fannin makamashi, musamman aikin bututun iskar gas na Trans-Sahara, wato TSGP.

Ziyarar na zuwa ne a daidai lokacin da dangantakar Aljeriya da Nijar ke kara karfi, musamman a fannin mai da iskar gas. A yayin ziyarar, Mohamed Arkab zai duba yadda ayyukan hadin gwiwar kasashen biyu ke tafiya, tare da mai da hankali kan ci gaban aikin TSGP.

Daga cikin abubuwan da za a duba akwai manyan ayyukan gyaran da ake gudanarwa a matatar man Zinder da ke Nijar, da kuma ci gaban aikin bututun iskar gas na Trans-Sahara.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted