Ministan harkokin wajen kasar Sin ya kai ziyara hedkwatar kungiyar tarayyar Afirka ta AU, da kasashen Habasha, da Tanzania, da Lesotho, Ziyararsa ta sake tabbatar da al’adar kasar Sin a fannin diplomasiyya, dama ministan ya kan kai ziyara nahiyar Afirka a farkon duk shekara. Yanzu haka an kwashe shekaru 36 ke nan wannan al’ada tana gudana
Minista Wang Yi ya yi tsokaci kan dalilin kasar Sin na ci gaba da wannan al’ada, inda ya ce, kasar Sin da kasashen Afirka suna da abokantaka mai zurfi da dogon tarihi, don haka, ya kamata a karfafa wannan hulda da kasashen Afirka a farkon duk shekara, A zahiri, wannan ziyara da mista Wang Yi ya yi, ta nuna dorewar manufar kasar Sin ta fuskar hulda da kasashen Afirka, da hadin kan kasashe masu tasowa a duniya, gami da dora harsashi ga karin hadin gwiwar bangarorin china da Afirka a shekarar da muke ciki.
A yayin ziyararsa a nahiyar Afirka, ministan wajen kasar Sin Wang Yi ya jagoranci taron tattaunawar bangarorin Sin da Afirka kan manyan tsare-tsare, a hadin gwiwarsa da Mahmoud Youssouf, shugaban kwamitin kungiyar AU, inda dukkan bangarorin 2 suka jaddada bukatar karfafa yin aiki tare don kare hakkin Sin da Afirka, da tabbatar da zaman lafiya da ci gaba a duniya.