Dan Siyasar Sweden Mai Kyamar Musulunci Ya Sake Wulakanta Kur’ani Mai Tsarki A Denmark

La’anannen dan siyasar Sweden din nan mai kyamar addinin Islama, Rasmus Paludan, ya sake tozarta kur’ani mai tsarki a birnin Copenhagen na kasar Denmark. Paludan

La’anannen dan siyasar Sweden din nan mai kyamar addinin Islama, Rasmus Paludan, ya sake tozarta kur’ani mai tsarki a birnin Copenhagen na kasar Denmark.

Paludan mai shekaru 43 shugaban jam’iyyar adawa ta kasar Denmark Stram Kurs, ya sake haifar da cece-kuce ta hanyar aikata wannan aika aika a wajen ofishin jakadancin Turkiyya da ke Denmark.

Wani faifan bidiyo da aka watsa a dandalin sada zumunta ya nuna Paludan yana wulakanta kur’ani mai tsarki, matakin da ya yi matukar bakanta ran musulmin duniya.

Matakin na Paludan ya zo ne bayan kisan da aka yi wa wani dan kasar Iraki mai suwan Salwan Momika wanda ya walakanta Al’Kur’ani a gidansa da ke birnin Sodertalje a ranar 30 ga watan Janairu.

Matashin mai shekaru 38 da haifuwa ya gudanar da kone-kone da tozarta littafin na Islama da dama a kasar Sweden a shekarar 2023.

Shi ma Paludan, ya shahara da tsokanar addinin musulmi ta hanyar kona kwafin kur’ani mai tsarki a kasashen Sweden da Denmark.

Kotun birnin Copenhagen a ranar 22 ga watan Nuwamban shekarar da ta gabata ta yanke wa dan siyasar mai ra’ayin rikau hukunci bayan ta same shi da laifin nuna wariyar launin fata dangane da furucin da ya yi yayin wata zanga-zanga a shekarar 2019.

A farkon wannan watan ne aka yanke wa Paludan hukuncin daurin watanni hudu a gidan yari a kasar Sweden saboda laifin yin batanci ga musulmi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments