Dalibai 27 Ne Suka Mutu Wasu Kuma Suka Jikkata A Pakistan

kimanin dalibai 27 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu a dama kuma suka jikkata bayan riftawar rufin gini a garin peshavar na pakistan

Rahotanni sun bayyana cewa akalla daliban makaranta  27 ne aka tabbatar da mutuwarsu yayin da wasu gwammai kuma suka jikkata bayan da rufin wata makaranta ya rufta a kasar Pakistan, kuma ta yi gargadi game da yiyuwar karuwar adadin wadanda suka mutu, a ci gaba da kokarin da ake yi na zakulo wadanda abin ya shafa a cikin burabutsan gini.

Wannan hadarin ya faru ne a wata makaranta mai zaman kanta ta alkhair education center a arewa masu yammacin kasar Pakistan a birin preshavar a yau alhamis, kamar yadda kakakin shugaban Asibitin na peshavar yace akwai dalibai guda 47 da suka jkkata a waje da lamarin ya faru.

Wani ma’aikacin agaji mai suna Bilal Ahmed ya bayyanawa manema labarai cewa ruwan sama ne aka yi kamar da bakin kwarya da ya haddasa ruftawar rufin gine-gine guda biyu na azuzuwan  makarantar,

Anashi bangaren mataimakin fira ministan kasar Pakistan Ishaq Dar ya fadi a cikin shafinsa na X cewa ruftawar rufi a wata makaranta a birnin peshavar ya jefa alummar kasar cikin matsanancin jimami don haka ina mika ta’aziya ga iyalan wadanda abin ya shafa, kuma tuni gwamnatin kasar ta dauki matakin gaggawa kan abin da ya faru

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted