Dakarun Yemen Sun Kaddamar Da Wani Sabon Hari Kan Haramtacciyar Kasar Isra’ila

Dakarun kasar Yemen sun sanar da kai hari kan birnin “Eilat” na haramtacciyar kasar Isra’ila da wani sabon makami Dakarun kasar Yemen sun sanar da

Dakarun kasar Yemen sun sanar da kai hari kan birnin “Eilat” na haramtacciyar kasar Isra’ila da wani sabon makami

Dakarun kasar Yemen sun sanar da cewa: Sun kai hari kan yankin Umm al-Rashrash da ke haramtacciyar kasar Isra’ila da makami mai linzami mai suna “Palastinu”, wanda rundunar sojin Yemen ta sanar a ranar Litinin.

Kakakin rundunar sojojin kasar ta Yemen Birgediya Janar Yahya Sare’e ya bayyana cewa: A ci gaba da taimakawa al’ummar Falasdinu da ake zalunta da kuma mayar da martani ga laifukan da yahudawan sahayoniyya suka yi kan ‘yan gudun hijira a birnin Rafah na Zirin Gaza, sojojin Yemen sun kaddamar da farmaki da makami mai linzami kan sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila a yankin Umm al-Rashrash da ke kudancin Falasdinu da aka mamaye. Kakakin Rundunar Sojin ta Yemen ya tabbatar da cewa: Sun samu nasarar cimma burin da suka sa a gaba, kuma dakarun kasar Yemen na ci gaba da gudanar da ayyukansu na soji domin nuna goyon baya da tallafawa al’ummar Falastinu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments