Wani babban jami’I a kungiyar ansarullah ta kasar yamen ya bayyana cewa dakarun sojin kasar suna yakin samar da makoma ne da kasar saudiya , kuma idan kasar saudiya ta fadada yakin to zai kara tsananta munanan hare haren mayar da martani da dakarun kasar yamen za su kai .
Haka zalika yayi kira ga kasashen turkiya da Pakistan da su lura da gargadin da shugaban kungiyar ansarullah abdulmali al-huthi yayi da su nisanta kansu daga shiga yakin da kasar Saudiya ta kaddamar akan alummar kasar yamen, idan ba haka ba za su yi mummunan asara. kuma illar hakan zata ci gaba da binsu na tsawon shekaru.
Wannan bayanin yazo ne bayan kashe fararen hula guda 6 tare da jikkata wasu guda 8 sakamakon harin da jiragen yakin saudiya suka kai kan gidajen fararen hula a lardin Taiz dake kudu maso yammacin kasar yamen
Yace yazuwa yanzu yakin da saudiya ta kaddamar kan kasar yamen yayi sanadiyar mutuwar dubban mutane amma har yanzu bata iya cimma burinta ba na kafa gwamnatin da take so da za ta kare manufofinta.ta zama yar amshin shata.