Rundunar Tsaron Juyin Juya Hali ta sanar da harbo wani jirgin sama mara matuki ciki kirar MQ-1 a gabashin mashigar ruwan Hormuz
Rundunar Tsaron Juyin Juya Halin Musulunci ta (IRGC) ta sanar da kamewa da kuma kakkabo wani jirgin sama mara matuki ciki kirar MQ-1 a gabashin mashigar ruwan Hormuz.
Ofishin hulda da jama’a na rundunar tsaron IRGC ya bayyana cewa: Jirgin sama mara matuki ciki na hudu da aka kame a kwanakin baya-bayan nan a gabashin mashigar ruwan Hormuz an harbo shi ne ta hanyar tsarin tsaron sararin samaniya na rundunar sararin samaniya ta rundunar IRGC.