Dakarun na “Kassam” Sun yi wa ayarin sojojin Isra’ila na kasa da suka nufi sansanin ‘yan hijira na Jabaliya, kwanton bauna, tare da bude musu wuta da hakan ya yi sanadiyyar mutuwar da dama daga cikinsu. Bugu da kari dakarun na “Kassam” sun kuma kai hari akan wasu sojojin da su ka zo ceton wadanda aka rutsa da su tun da fari, da hakan ya kara yawan wadanda su ka halaka.
Bayan da sojojin da su ka saura, su ka gudu zuwa wani kango domin buya, dakarun na “Kassam” sun kai musu yaki a kusa da kusa inda su ka bude musu wuta gaba da gaba tare da jefa musu nakiyoyi da hakan ya yi sanadin kashe da jikkawa da dama daga cikinsu.