Dakarun rundunar “Shahid Izzuddin al-kassam’ da kuma ” Sarayal Kuds” sun sanar da kai jerin hare-hare akan sansanonin ‘yan sahayoniya a yankuna mabanbanta na Gaza.
A bayanin da dakarun ” Kassam” su ka fitar sun bayyana hare-hare masu yawa da su ka kai wa ‘yan mamaya, da su ka hada da tarwatsa motocin buldoza biyu samfurin D9 a unguwar Zaituna a cikin birnin Gaza.
Haka nan kuma sun kai wani harin a ranar 6 ga watan Yuli wanda su ka rusa tankar yaki ta “Mirkava” ta hanyar amfani da wata nakiya mai tsananin fashewa.
Bugu da kari , Kassam ta ce a ranar 9 ga watan Yuli din ta kai wani harin akan sansanin da kwamandoji masu bayar da umarnin yaki suke a gabashin unguwar ‘al-tuffah’ a gabashin birnin Gaza,wanda ya yi wa abokan gaba asara mai yawa.
Haka nan kuma maharban na Kassam sun yi nasarar harbe wani sojan HKI a yankin Abasan al-kabirah, a gabashin birnin Khan-Yunus dake kudancin Gaza.
Su ma dakarun ” Sarayal-Kuds” na kungiyar Jiahdul-Islami sun sanar da jerin hare-hare akan sansanoni mabanbanta na ‘yan sahayoniya da su ka hada da rusa motocin yaki irin su tankar “Mirkava’ a unguwar ‘ al-Tuffah’ a cikin birnin Gaza. Haka nan kuma dakarun sun sanar da rusa wata motar ta soja a cikin Gaza.