Dakarun kare juyin juya halin musulunci na kasar Iran wato IRGC sun rubuta budaddiyar wasika ga Amurkawa wadda a cikinta suka bukavesu su farka su kuma kama gaban yan siyasarsu masu cin hanci da rasha da kuma lalata dunkiyar kasarsu a yake yaken da basa da amfani.
Tashat talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto budaddiyar wasikar, wacce take magana kai tsaye ga Amurkawa ba tare da ta biyo da gwamnati ko kuma kafafen yada labaran kasar ba, bayan watanni kimani 7 na fafatawa da sojojin Amurka da HKI da kuma nasarar da Iran ta samu a kan sojojin amurka a yankin yammacin Asia da kasha 1% na abinda Amurka take kashewa yake yake a duniya a shekara guda.
Sojojin Amurka sun kashe Jagoran juyin juya halin musulmi Imam Khaminaei (q) da iyalan gidanda a rana ta farko sannan suka kashe yan makarantar Minab a rana ta biyu. Banda haka suka lalata asbitoci da makarantu da kuma kashe yan wasa da kuma fararen huka wadanda basu san hawa ko sauka ba.
IRGC ta bukaci Amurkawa sun kawo karshen sansanonin sojojin kasar har 800 da suke da shi a duk fadin duniya, su kuma kawo karshen dangantaka da HKI wacce bata kawowa kasar in banda musibu wadanda basa karewa. Tace su yi sauri su dawo da kasarsu daga hannun yan siyasa wadanda suke son wargazata.