Dakarun IRGC Sun Kashe Yan Ta’adda 12 A Lardin Sistan Baluchistan

Dakarin kare juyin juya halin musulunci (IRGC) a kudu maso gabacin kasar Iran sun wargaza tawagar yan ta’adda guda biyu suka kuma halaka 12 daga

Dakarin kare juyin juya halin musulunci (IRGC) a kudu maso gabacin kasar Iran sun wargaza tawagar yan ta’adda guda biyu suka kuma halaka 12 daga cikinsu a yankin Sistan Baluchistan.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto dakarun tare da taimakon wasu bangarorin Jami’an tsaron sun fatattakin gungun yan ta’adda har guda biyu  sannan sun kashe yan ta’adda har guda 17 a cikinsu.

Labarin ya kara da cewa sun twace boma-bomai wadanda ake iya tadasu daga nesa har 25. Da remote control, da wasu kayakin aikin soje da dama daga hannunsu a garin Chabahar.

Sannan a wani aikin soje da suka aiwatar a yankin Sistan da Baluchestan, sun kama yan ta’adda guda 6 bayan sun gano mabuyarsu. Wadannan yan ta’addan sun saba shigowa kasar Iran daga Afganisatn da kuma Pakisatin. Inda suke shigoda muggan kwayoyi ko kuma su aiwatar da ayyukan ta’addanci.

Har’ila yau yan ta’adda masu kafirta musulmi suna shigowa wannan yankin, inda suke fafatawa da Jami’an tsaron kasar Iran.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments