Rundunar Tsaron Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran ta jaddada cewa: Babu tsaro a yankin Gabas ta Tsakiya ba tare da tsaron Iran ba
Mataimakin kwamandan hedikwatar tsakiya ta Khatamul-Anbiya da ke Iran, Birgediya Janar Kioumars Heidari, ya yi gargadin cewa: Duk wani hari da za a kai wa yankin Iran zai fuskanci mayar da martani mai tsauri, yana mai jaddada cewa: Tsaron yankin ba shi da ma’ana idan ba tare da tsaron Iran ba.
Birgediya Janar Heidari ya bayyana cewa: Sanya tsaron Iran cikin hatsari yana nufin babu mafaka ga Amurka, Isra’ila, da kawayensu a yankin. Ya kuma bayyana tura kayan aikin soja da jiragen ruwa na Amurka a Tekun Farisa a matsayin kuskure, yana mai gargadin cewa ci gaba da wannan hanya zai haifar da shan kaye ga Amurka da kuma tilasta mata ficewa daga yankin babu shiri.
A nasa bangaren, Babban Kwamandan Rundunar Tsaron Cikin Gida ta Iran, Birgediya Janar Ahmad Reza Radan, ya tabbatar da cewa: Masu tsaron kan iyaka a halin yanzu suna kan kololuwar karfinsu da shirye-shiryensu, yana mai gargadin Amurka da ‘yan Sahayoniyya game da duk wani kuskure da aka yi.
A yayin wani biki na girmama kwamandan rundunar tsaron kan iyaka, yayin da yake tunawa da shahidan juyin juya halin Musulunci, tsaron kasa mai alfarma, da kuma shahidan yakin da ‘yan Sahayoniyya suka kawo Iran da kuma tawaye da aka yi kwanan nan, Radan ya lura cewa gwamnatin Iran ta dogara ne da mutanen da suka sadaukar da rayukansu don kare ta, wanda hakan ya taimaka wajen dakile yunkurin makiya a lokacin rikicin da ya faru kwanan nan.