Dakarun Izzuddeen Al-Qassam bangaren sojin kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas suna ci gaba da arangama da tunkarar yahudawan sahayoniyya ‘yan ta’adda
Dakarun Izzuddeen Qassam bangaren sojin kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas suna ci gaba da gwabza fada tare da tunkarar sojojin yahudawan sahayoniyya da ke kutsawa cikin yankuna da dama na Zirin Gaza, lamarin da ya zuwa yanzu ya yi sanadin halakar daruruwan hafsoshi da sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila, baya ga raunata wasu dubun-dubatar sojojin gami da tarwatsa daruruwan motocin yakin ‘yan mamayan.
Har ila yau ‘yan gwagwarmayar Al-Qassam sun bayana cewa: Dakarunta sun yi wani kazamin artabu da sojojin mamayar yahudawan sahayoniyya da suka kutsa cikin yankuna da dama na garin Tubas da ke gabar yammacin kogin Jordan da aka mamaye.
Haka nan kafofin yada labaran ‘yan gwagwarmaya sun wallafa hotunan hare-haren da ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa suka kai wa sojojin yahudawan sahayoniyya da suka yi kawanya ga asibitin “Indonesiyan da ke unguwar Tal Al-Sultan, a yammacin birnin Rafah, a kudancin zirin Gaza.