Tun gabanin Hizbullah ta sami isasshen lokacin da za ta yi nazarin yadda ya kamata girman taya Gaza fada ya kasance, ta bude fagen daga da Haramtacciyar Kasar Isra’ila. Rana daya ce a tsakanin farmakin guguwar Aksa, 7 ga watan Oktoba 2023, da fara kai wa sansanonin Haramtacciyar Kasar Isra’ila hare-hare da Hizbullah ta yi.
Aliyul Fawwaz a cikin makalar da ya rubuta a shafin Almayadin ya bayyana cewa: “Hizbullah ce ta farkon a tsakanin kungiyoyin gwagwarmaya da ta amsa kiran kwamandan dakarun “Kassam” Muhamamd Dhaif da kuma na sauran kwamadojin rundunar da ya biyo baya.”
A zangon farko, Hizbullah ta takaita kai hare-hare akan sahun farko na sansanonin ‘yan mamaya da suke kan iyaka saboda cimma manufofi biyu a lokaci daya: Hana ‘yan mamaya amfani da dukkanin karfinsu akan Gaza, wato a raba musu hankali biyu,sannan kuma a lokaci daya ba a bude yaki gadan-gadan da sub a, domin kare kasar Lebanon daga fuskantar munanan hare-haren ‘yan sahayoniyar.
Lamari ne mai cike da sarkakiya domin a fili yake cewa lokacin da Hamas ta yanke shawarar kai wancan farmakin ba ta shawarci daya daga daga cikin sauran ‘yan gwgawarmaya ba, ko kuma sanar da su.
Daga baya shugaban shahidar al’umma, Sayyid Hassan Nasrallah, da kuma jagoran juyin musulinci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamnei sun bayyana cewa; ko kadan ba su da masaniya akan cewa za a kai wannan farmakin.
Sai dai kuma hakan bai hana su yin duk abinda za su iya yi ba domin shiga cikin fadan da taimaka wa Falasdinawa ‘yan gwgawarmaya.
A cikin hanyoyin sadarwa na al’umma wani bidiyo ya rika kai da komowa wanda yake nuna kwamandan mayakan Hizbullah Ibrahim Akil ( bayan shahadarsa) yana cewa: “ Nauyi ne na shari’a da yake a wuyan Hizbullah ta taimakawa Gaza, kuma da a ce lokaci zai koma baya, to da za mu sake maimata hakan”. Ya kuma ce, “wajibi ne a bisa mizani na shari’a Hizbullah ta yi abinda ta yi na taya Falasdinu gwgawarmaya. Domin baya halarta a zuba idanu ana ganin yadda Isra’ila take kashe dubun dubatar Falasdinawa a Gaza.
**
Tun farkon fari, ma’auni na sharia da ‘yan’adamtaka su ne su ka sa Hizbullah shiga cikin taimakawa Falasdinawa fada, ba wai wani ma’auni na siyasa zalla ba. Batu ne na addini da kyawawan halaye da ‘yan adamtaka. Awajen yin hakan kuwa kungiyar ta sadaukar da kai da yawa, da biyan farashi mai tsada.
Shi abu ne mai yiyuwa a kaucewa hakan?
Za a iya cewa a tsawon watannin farko na shiga yaki da Haramtacciyar Kasar Isra’ila da Hizbullah, ta bude watse shirye-shirye na wayar da kai ga magoya bayanta gabanin waninsu akan dalilin da ya sa ta shiga wannan yakin.
Abu mai muhimmanci shi ne cewa,zabin da Hizbullah ta yi na shiga wannan yakin yana da halarci na shari’a da ‘yan adamtaka. Ba kuma hakan yana nunfin cewa zai hana Haramtacciyar Kasar Isra’ila kai wa Lebanon,musamman Hizbullah hari ba, da za ta kira shi na kariya. Watakila wasu su ce idan Hizbullah ta jira sai an kawo wa Lebanon hari sannan ta mayar da martani, da zai fi zama karbabe, a kalla a wurin mutanen cikin gida. Wasu mutanen Lebanon za su fi amincewa da ace Hizbullah ta shiga yaki ne domin kare Lebanon ba domin kare Falasdinu ba.
Sai dai kuma a fili yake ce ga masu adawa da Hizbullah da gwagwarmaya ba ruwansu da a kowane yanayi ne yaki ya barke. Za su cigaba da dorawa Hizbullah laifin cewa ta jafa kasar cikin yaki.
Dama ko kadan mutane irin wadanan ba su taba bai wa gwagwarmayar Hizbullah gaskiya ba.
Sai dai kuma da ace Hizbullah ba ta shiga cikin taya Gaza da gwgawarmayar Falasdinawa fada ba, to da farashin da za ta biya sai ya fi wanda ta biya, bayan shigarta.
Sakamakon Farko:
Gaskiyar da aka san Sayyid Hassan Nasarallah da ita, da kuma tsayuwarsa a kanta, za ta mutu a cikin zukatan falasdinawa. Amma a yanzu ana daukarsa a matsayin wanda ya yi shahada saboda Falasdinu.
Dhaif ya kira yi ‘yan gwgawarmaya da cewa: “Ya ku ‘yan’uwanmu ‘yan gwgawarmaya a Lebanon, Syria Iraki da Iran, Wannan ce ranar da dukkanin fagagen gwgawarmaya za su hade a wuri daya a fafata.”
Sannan kuma ya kira yi dukkanin al’ummar musulmi da cewa:
“ Ya ku ‘yan’uwanmu a Jordan, Lebanon,Masar, Aljeriya, da larabawan Yamma.(Arewacin Afirka,). Da kuma Pakistan, Malyasia da Indonesia da dukkanin kasashen larabawa da na musulmi, ku fara yunkurawa a yau ba sai kun jira zuwa gobe ba, zuwa Falasdinu.”
Tare da cewa Hizbullah ta amsa wannan kiran tun a tashin farko, sai dai wannan bai hana ‘yan adawa na kusa da nesa, da ma a cikin masu kishin musulunci sukarta ba.
Kafafen sadarwa na jama’a- kamar yadda ake kiransu-, na gaskiya da na bogi, da masu alakanta kansu da addini da wadanda kungiyoyin leken asiri ne suke tafiyar da su, sun rika kaskantar da shigar Hizbullah cikin yakin. Suna nuna cewa abinda take yi, wasan kwaikwayo ne kawai. Tana kakkabo da lalata sandunan dake dauke da na’urorin leken asiri akan iyaka, amma duk ba su ganin muhimmancin abinda take yi. Domin tana dode idanuwan Isra’ila ne na leken asirin a cikin Lebanon har zuwa cikin Syria, da ma Turkiya,amma wadannan ‘yan adawar idanunsu sun rufe. Suna cewa wai tana kai wa dirkoki hari.!
Yanzu mu sauya yadda hoton lamarin yake; mu dauka cewa Hizbullah ta takaita kai hare-harenta ne kawai a cikin yankin “Mazari’u-Shib’ah” da “ Tuddan Kafar-Kilah” da na Lebanon ne Isra’ila take mamaye da su. Da idan wannan abinda ya faru, to da masu adawa da Hizbullah a tsakanin masu ikirarin addini sun tsananta farfaganda da bakanta sunan gwgawarmayar ta Lebanon.
Sakamako Na Biyu:
Idan ace Hizbullah ba ta shiga taya mutanen Gaza yaki ba, to da an koma bankado tarihin yakin bassar Syria an yi amfani da shi a matsayin makami akan Hizbullah! Za kuma a share fagen wata sabuwar fitina anan gaba.
Wadannan mutanen za su mayar da ‘yan ta’addar Da’seus ( ISIS) jarumai da cewa; Hizbullah ta yaki Ahlussunah a Syria, yanzu kuma ta ki taimakon Falasdinawa. Da kuma sun kara da cewa Hizbullah karyar gwagwarmaya take yi, domin ga lokacin gwgawarmaya ya zo, amma ta noke.!
Akan haka za su gina wata sabuwar fitina a tsakanin Hizbullah da Hamas, da kuma a tsakanin shia da Sunna.
Wani abu mai jan hankali anan shi ne da ace Hizbullah ba ta shiga cikin wanann fadan ba, to babu abinda zai hana Isra’ila ta akfa mata da yaki idan t agama da Hamas.
Kuma da shigar Hizbullah yakin da irin sadaukarwar da ta yi mai girma, bai hana masu mugun nufi, cigaba da fesa dafinsu na bangaranci ba. Idan da hakan ba ta faru ba, to da tasirin dafin da za su feso sai ya fi na yanzu illa da kisa.
Sakamako Na Uku:
Da akwai banbanci ace Isra’ila ta shammaci Hizbullah da yaki, idan da ba ta shiga taimakawa Gaza ba, da kuma ace ta shiga cikin yakin ta kaddamar zababbun samarinta da jagororinta ba,su ka zama shahidai akan hanyar Kudus. Musamman a wannan lokacin da kasashen musulmi da Larabawa su ka yi zaman dirshen suna kallo ana yanka alummar Falasdinu dare da rana, a cikin ranaku da kwanakin shekara guda, da watanni biyu babu kakkautawa.
Ta fuskar gwagwarmaya, wannan batu ne mai muhimmanci,domin matsayar da Hizbullah din ta dauka na tarihi ne da kuma kyawawan halaye. Zai kuma shiga cikin tarihi da zukatan al’umma.
Sakamako Na 4:
Da ace Hizbullah ba ta shiga cikin taimakon Falasdinawa ba, to da an mance da cewa; Muhmmad Dhaif ya kirayi dukkanin al’ummar musulmi ne su taimakawa gwagwarmaya, sai a mayar da hankali akan cew Hizbullah ba ta karba kiran ba. Ba za a tuna da yadda sauran kasashen musulmi su ka zama ‘yan kallo ba sai ta kadai.
Sakamako na 5:
Shahadar Sayyid Hassan Nasrallah tare da sauran jagororin kungiyar Hizbullah, zai taka rawa wajen rage ruruwar wutar fifitar bangaranci a tsakanin shia’ da sunna. Domin kuwa a tsawon shekara da shekaru Amurkawa da Isra’ila kawayensu sun kashe makudan kudade domin haddasa wannan fitina. Da Hizbullah ba ta shiga cikin fadan Gaza ba, to da ‘yan sahayoniya da Amurkawa sun cimma wannan manufa cikin sauki.
Da kuma ace Hizbullah ba ta shiga cikin yakin Gaza ba, to da an rasa kyakkyawan misali na sadaukar da kai na koli a tsakanin al’umma a cikin shekatun nan da ma masu zuwa a nan gaba.