Mutane 27 ne suka mutu sakamakon kamuwa da cutar amai da gudawa a birnin Kassala na kasar Sudan, wanda ke cike da jama’a da ‘yan gudun hijira
Rahotonnin baya-bayan nan kan halin da ake ciki a kasar Sudan suna nuni da cewa: An samu sabbin mutane da yawansu ya kai 49 da suka kamu da cutar kwalara a jihohi biyar, wanda ya kawo adadin wadanda suka kamu da cutar suka haura zuwa 556, ciki har da mutuwar mutane 27.
Daruruwan mutane da suka kamu da cutar da suka hada da aƙalla mutuwar mutane 30, adadin farko na cutar kwalara a cikin kimanin makonni 3 kacal ya bazu cikin sauri a cikin jihohi 5 na Sudan sakamakon rashin ƙarfi na yanayin harkar kiwon lafiya da na muhalli a waɗannan yankuna. Kashi 90 cikin 100 na al’amuran sun faru ne a Jihar Kassala da ke Gabashin kasar wanda ke cike da dubban ‘yan gudun hijira.
Ministan lafiya da ke kula da jihar Kassala Ali Adam ya shaida wa tashar talabijin ta Al-Alam cewa: Halin da ake ciki yanzu haka an fara samun daidaiton al’amura, amma jihar Kassala da yanayin da kasar ke ciki gaba daya yana ci gaba da haifar da matsaloli a dukkan bangarorin rayuwa, inda ake fama da yawan mutanen da suka rasa matsugunai, bullar yaƙe-yaƙe a jihohi da kwarara ‘yan gudun hijira daga nan zuwa can.