Shugaban kasar Colombia Gustavo Petro ya gargadi kasashen Latin Amurka dangane da kasar Amurka, ya kumabukacesu da su hada kansu ko kuma za’a maidasu bayi a kasashensu.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakaltoPero yana fadar haka bayan da shugaban kasar Amurka Donal Trump ya zargi Petro da fasa korin miyagun kwayoyi zuwa Amurka shima irin zargin da yayiwa Madoro kafin a kama shi a birnin Caracas a ranar Asabar da ta gabata.
Shugaba Trump ya bayyana cewa yana iya yiwa shugaban Colombia irin abinda yayiwa Madoro ne a jiya lahadi a lokacinda yake cikin jirginsa na shugaban kasa ‘Airforce One’.
Shugaban ya bayyana Venezuela da Colombia a matsayin kasashen da basa da lafiya, a kuma nan ba da dadewa ba zai yi maganin kasashen biyu.
A wani sakon da ya aika a shafinsa na X shugaba Petro nakasar Colombia ya bayyana cewa Amurka ce kasa ta farko a duniya wacce ta kaiwa babban kasar wata kasar Laten Amurka, wato Caracas na kasar Venezuela.
Trump dai yace kasar Amurka ce take iko da kasar Venezuela duk da cewa kotun koli na kasar ta maye gurbin shugaba Madoro da mataimakiyarsa Delcy Rodriguez a matsayin shugaban rikon kwarya. Kuma yayi barazanar aiko sojoji zuwa kasar Iran gwamnatin kasar Venezuela bata yi abinda ya dace ba.
Kafin haka Maco Robio sakataren harkokin wajen kasar Amurka ya ja kunnen shugabannin Venezuela su dauki matakan da suka dace na hada kai da Amurka ko kuma su fuskanci karin hare-haren sojojin Amurka. Karin matsin lamba na tattalin arziki da siyasa.