CNN:Trump Ya Yi Wa Ukiraine Barazana

Tashar talabijin din CNN ta Amurka ta bayar da labarin cewa; Shugaban kasar Amurka Donald Trump y ayi wa takwaransa na kasar Ukiraine barazana akan
tambarin cnn

Tashar talabijin din CNN ta Amurka ta bayar da labarin cewa; Shugaban kasar Amurka Donald Trump y ayi wa takwaransa na kasar Ukiraine barazana akan ci gaba da kai wa masana’antun man fetur na Rasha hari.

Gwamnatin ta Donald Trump ta ce za ta dakatar da bai wa Ukraniya bayanan sirri matukar ta ci gaba da kai wa cibiyoyin makamashi na kasar Rasha hare-hare.

Rahoton na tashar talabijin din CNN ya kuma ci gaba da Amurka gwamnatin ta Trump ta kuma yi wa shugaban  Ulkiraniya Zylanesky barazanar cewa za ta dakatar da sayarwa kasashen turai makaman da suke ba shi yana yaki da su.

Rahoton ya kuma ce; Donald Trump ya kawo iya wuya da shugaban Ukiraniya saboda kasarsa ba ta ganin kima da darajar taimakon da Amurkan take ba shi.

Trump dai ya cimma yarjejeniya da Rasha akan dauke mata makamai ta fuskar makamashi musamman Disel, da yake son ganin ya shiga kasuwannin Amurka.

Wannan yarjejeniyar dai ta bakantawa kasashen turai da kuma Ukiraniya, saboda suna daukarta a matsayin yankan baya.

Amurka da kawayenta na turai sun kakabawa Rasha takunkumin sayar da makamai saboda yakin Ukiraniya. A wannan tsakanin kasashe na turai sun koma sayen makamashi mai tsada daga Amruka.

A halin yanzu da mashigar Ruwan Hurmuz ta zama a rufe, Amurka ta kulla wannan yarjejeniyar da Rasha ba tare da tuntubar kasashen na turai ba, lamarin da ya kara sabanin dake tsakanin gwmanatin Donald Trump da kasashen yamma.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted