Al’ummar Gaza na cikin Mawuyacin Hali na Rashin Kayan Bukatar Rayuwa

Ma’aikatar Lafiya ta Gaza ta yi gargaɗi kan cewa asibitocin birnin za su daina aiki na da sa’o’i 48 sakamakon rashin man fetur. A wata

Ma’aikatar Lafiya ta Gaza ta yi gargaɗi kan cewa asibitocin birnin za su daina aiki na da sa’o’i 48 sakamakon rashin man fetur.

A wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar, ta yi gargaɗi kan cewa “sauran asibitoci da cibiyoyin lafiya da cibiyiyoyin samar da oxygen za su daina aiki nan da sa’i’o’i 48.”

Ma’aikatar ta ce sakamakon hana shigar da man fetur cikin birnin wanda da shi janaretocin asibitocin ke aiki, shi ya janyo hakan.

Baya ga man fetur, kayan abinci da magunguna na daga cikin ababen da Isra’ila ta saka takunkumin hana shiga da su Gaza.

Harin da jiragen yakin Isra’ila suka kai da sanyin safiyar Lahadi sun kashe Falasdinawa bakwai tare da jikkata wasu da dama a Gaza.

Hare-haren sun faɗa kan gidaje a Rafah da birnin Gaza, inda aka samu asarar rayukan fararen hula da suka haɗa da kananan yara kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Wafa ya ruwaito.

Haka kuma makaman atilari sun yi luguden wuta a kudancin Rafah da tsakiyar Gaza, da kuma a birane da ke gabashin Khan Yunis. A unguwar Daraj da ke Gaza, farar hula ɗaya ya rasu da dama kuma sun jikkata a wani hari da sojojin na Isra’ila suka kai wani gida.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments