Shugaban marasa rinjaye a majalisar dattawan Amurka chuck Schumer ya yi suka mai tsanani game da harin soji da shugaban Amurka Donald Trump ya kai wa kasar Iran ba tare da wani izini ba, kuma ya kirashi da yakin da ya saba ma doka, da aka yi faduwar totuwa a cikinsa da kuma jefa rayukan Amurkawa a cikin hadari tare da kara jawo hauhawan farashi da kara jefa talaka cikin tsadar rayuwa
A cikin wani bayani da ya wallafa a shafinsa na X ya ce Donald Trump ya jefa mu cikin haramtaccen yaki kuma ya sha kashi a yakin da ya kaddamar, da ya rasa mafita a cikinsa, ya ce rashin sanin dabarun yaki da rashin da’a da kuma rashin kyakkyawar shawara ta gaskiya ya jefa sojojinmu cikin hadari da kuma kara farashi a kullum ga amurkawa, jagorancin trump babban gazawa ne, dole ne mu kawo karshen wannan yakin mu fara gyara barnar da yayi,
Wannan bayani yana zuwa ne adaidai lokacin da gwamnatin trump take ci gaba da shan kaye a yakin da ta kaddamar kan kasar iran ba tare da amincewar majalisa ba a farkon wannan shekara ya hada kai da gwamnatin HKI.
Yace duk da kwashe watanni yana kaddamar da hari da kuma yin barazana ga kasar iran amma ta tsaya kyam wajen kare mutunci da martabar kasarta inda dakarun gwagwarmaya kasar iran suka jawo mummuna asara ga masu kai mata hari.