mataimakin jakadan kasar china na dindidin a majalisar dinkin duniya SUN Lei yayi kira da a girmama hakkin iran da doka ta bata na amfanin da makamashin nukiliya domin ayyukan zaman lafiya, a lokacin da suka hau kujerar naki ita da kasar rasha a kudurin da kasar Amurka ta gabatar a gaban kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya kan kasar Iran
a ranar 17 ga watan satumba kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya ya kasa amincewa da kudurin sake sabunta wa’adin aikin tawagar kwararru ta majalisar dake da alhakin sa ido kan yadda ake aiwatar da takunkuman da aka sake kakabawa iran ta hanyar tsarin da aka fi sani da Snapback mechanism a shekara ta 2025 , kudurin ya samu kuriu 11 na amincewa, biyu na kin amincewa daga china da rasha sai kuma kasashe biyu da suka ki kada kuri’a
Sun yace baijin ta kada kuri’a kin amincewa da kudurin ne da nufin barin kokarin diflomasiya da ake yi na ganin an warware takaddamar da ake yi kan shirin nukiliyar iran ta hanyar tattaunawa , kudurin an gabatar da shi ne don kara tsawaita lokacin kwamitin mai lamba 1737 kan takunkumin da aka sake sanyawa iran har zuwa watan satumbar shekara ta 2027 kafin ya kare