Yahudawa ‘yan share wuri zauna da ke yankunan Falasdinawa da Isra’ila ta mamaye, wato matsugunin Kibbutz Hanita, wanda ke kusa da yankin kan iyakar Lebanon, sun shigar da kara suna neman kimanin dala miliyan 11 daga Ballet Vision, asusun saka hannun jari na kasar China wanda ke kula da masana’antar Hanita Lenses, suna zarginsa da kin girmama tsarin saka hannun jari Kibbutz.
Karar, wacce aka shigar a Kotun Gundumar Tel Aviv, ta ce kamfanin Ballet Vision, wacce ke da kusan kashi 80% na Hanita Lenses, ya ki sayen hannun jarin kibbutz, duk da cewa an sanya wa’adin da aka kayyade a watan Disamba na 2025.
A cikin wata wasika da aka makala a cikin takardar, asusun ya ambaci takunkumin siyasa da na dokoki, yana mai cewa Beijing ta ayyana wadannan yankuna a matsayin “wurin da ke da babban hadari”.
Gwamnatin kasar Sin ta sanya Isra’ila a matsayin yankin da ke da babban hadari kuma ta haramta duk wani sabon shiri na zuba jari na kasar Sin ,” in ji asusun. “Muddin wannan takunkumin ya ci gaba da aiki, babu wata damar aiki ta zahiri a wannan yanki.