China Ta Kakaba Wa Kamfanonin Amurka 20 Takunkumai

Gwamatin kasar China ta kakaba takunkumai akan wasu kamfanonin Amurka 20 masu kere-kere a fagen tsaro, da kuma wasu manyan shugabanninsu 10. China din ta

Gwamatin kasar China ta kakaba takunkumai akan wasu kamfanonin Amurka 20 masu kere-kere a fagen tsaro, da kuma wasu manyan shugabanninsu 10.

China din ta dauki wannan matakin ne bisa cewa wadannan kamfanonin suna sayarawa da yankin Taiwan makamai.

Ita dai kasar China tana daukar  Taiwan a matsayin wani hanki na kasarta wanda ya fandare, don haka take kalubalantar kasashen waje da suke mu’amala da shi kai tsaye maimakon bi ta Beijin.

 A nata gefen ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta  yi suka akan  matakin na China wanda ya kunshi rike dukiyar da kamfanonin suke da shi a cikin China da kuma hana daidaikun mutanen China mu’amala da kamfanonin da kuma ma’aikatansu.

Takunkumin na Amurka ya kunshi hana shugaban kamfanin  “Anduril Industries” da wasu jami’ansa  9, shiga cikin kasar, haka nan sauran shugabannin kamfanonin.

A makon da shude ne dai Amurkan ta kulla yarjejeniyar sayarwa da Taiwan makamai da kudinsu ya kai dala biliyan 11.1, da shi ne cinki makamai mafi girma a tsakanin bangarorin biyu.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen China ya bayyana cewa; Batun Taiwan yana da matukar muhimmanci a wurin China, kuma jan layi ne wanda tsallake shi a alakar Washington da Beijin ba zai zama karbabbe ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted