Mai Magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar China ta bayyana cewa: Beijing ba ta lamunta da duk wani kokarin tsoma bakin kasashen waje a harkokin cikin gidan wannan kasar.”
Mao Ning wacce ta gabatar da taron manema labaru a brinin Beijing a kasar China ta yi kira ga kasar Amurka da ta fasa Shirin kai wa kasar Venezuela hari wanda ba ya kan doka,mai makon haka ta karfafa sulhu da zaman lafiya a cikin yankin Latin.
Kamfanin dillancin labarun Xin Hua na kasar China ya nakalto mai Mao Ning tana cewa; Kasar China ba ta kuma lamunta da kakaba wa kasar ta Venezuela takunkumi ta gefe daya wanda baya kan doka ba, kuma take dokokin kasa da kasa ne, saboda ba a yi shi a karkashin amincewar kwamitin tsaro na MDD ba.
Mao Ning ta kuma ce; Beijing tana son ganin dukkanin bangarori su girmama hurumin kasar Venezuela, su kuma kaucewa haddasa hargitsi.
A ranar 24 ga watan Nuwamba Amurka ta sanar da haramta wata kungiya wacce take mai fataucin muggan kwayoyi ce, kuma shugabanninta su ne shugaban kasar Venezuela Nicholas Maduro da kuma wasu jami’an gwamnatinsa.
Kasar Venezuela ta karyata abinda Amurkan ta riya, tare da bayyana shi a matsayin ‘karya bai sa dariya” sannan kuma tana son fakewa da haka ne domin tsama baki a harkokin cikin gidan kasar.
A cikin watannin bayan nan dai Amurkan tana kai hare-hare akan kananan jiragen ruwa a tekun Carrebea bisa riya cewa suna dauke da kwayoyi daga Venezuela zuwa Amurka.