Kasashen Chaina da Rasha sun fara atisayen soje na hadin giwa bayan barazanar kungiyar tsaro ta Nato karkashin jagorancin Amurka.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa an sayawa atisayen suna ‘Hadin giwa teku na 2024’ kuma an fara atisayen a garin Zhanjiang na lardin Guangdong a jiya Lahadi. Sannan wannan atisayen zai ci gaba har zuwa tsakiyar watan yulin da tsakiyar yuli.
Tashar talabijin ta CCTV ya bayyana ma’aikatar tsaron kasar Chaina na cewa a halin yanzu sojojin kasar Rasha suna iko da arewa maso yammacin tekun pecific, sannan wannan atisayen bai da nufin takalar wata kasa.
Labarin ya kara da cewa a cikin wannan atisayen za’a gwada makamai masu linzami kuma garkuwa ga makamai. Har’ila yau zasu gwada dabarbarun kare kai daga makamai dabam daban.
A ranar labaran da ta gabata ce a taron kasashen kungiyar tsaro ta NATO 32 a birnin Washington suka bayyana China a matsayin kasa wacce take taimakawa Rasha a yakin da suke fafatawa da ita a Ukraine. Kuma sun ware dalar Amurka biliyon 43 don taimakawa kasar ta Ukraine.