Gwamnatin Chadi ta yiwatsi da zargin da Nijar ta yi na kai mata hari da jirgin sama marar matuki a yankin Agadas a ranar 24 ga Oktoba.
A cikin wata sanarwa da aka karanta a talabijin na kasar, mai magana da yawun gwamnatin N’Djamena, Gassim Chérif Mahamat ya nemi shaida daga Yamai kuma ya sanar da cewa Gwamnatin Chadi na goyan bayan duk wani bincike na kasa da kasa mai zaman kansa kan lamarin.
Tunda farko dai Nijar ta zargi N’Djamena, tare da hadin gwiwa da Faransa, da kai harin wanda ya yi ajalin fararen hula biyu da raunata wasu a yankin Emilulu dake jihar Agadas.
Bayan ta yi Allah wadai da lamarin, gwamnatin Nijar ta sanar da matakai, ciki har da kiran jakadan Chadi dake kasar domin nuna fishi kan lamarin a hukumace..
Gwamnatin ta Nijar ta kuma yi Allah wadai da abinda ta danganta da aika-aikar ta’addanci, wanda ta ce ya keta hurumin kasar, da Dokar Majalisar Dinkin Duniya, da kuma ka’idojin kafa kungiyar Tarayyar Afirka (AU).”
Tuni Kuma ta shigar da kara gaban kwamitin tsaro na MDD da kuma na tarayyar Afrika tare da neman a gudanar da bincike na kasa da kasa.
Wannan sabon zargi ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun takun-tsaka tsakanin Yamai, Paris, da N’Djamena.
A ranar 2 ga Satumba, Kyaftin Roger Gabriel na Nijar ya ambaci wani shiri wanda ya shafi hukumomin Chadi da sojojin Faransa na musamman, dangane da yunkurin juyin mulki na ranar 28 zuwa 29 ga watan Agusta a Niamey.