Iran da Amurka sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ta mako biyu

Kasashen sun sanar da hakan ne a cikin daren ranar Laraba, gabanin wa’adin da shugaba Trump ya gindaya na kai munanen jerin hare hare kan
Iran da Amurka sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ta mako biyu

Kasashen iran da Amurka sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ta wucin gadi ta tsawon makonni biyu bisa sharadi.
Kasashen sun sanar da hakan ne a cikin daren ranar Laraba, gabanin wa’adin da shugaba Trump ya gindaya na kai munanen jerin hare hare kan cibiyoyin makamashin Iran, matakin da kasashen duniya da kungiyoyin kasa da kasa da dama sunyi ca akansa kan cewa hakan zai iya kasancewa laifin yaki.

Sakatariyar majalisar tsaron kasa ta Iran, ta bayyana cewa an cimma kusan illahirin manufofin yakin da aka kallafa wa kasar a watan Ramadan, kuma kasar za ta shiga tattaunawa da Amurka a cikin makon nan a birnin Islamabad na kasar Pakistan.

Iran ta bayyana tsagaitar da babbar nasara tana mai cewa hakan ya samu ne sakamakon juriya da kuma tsayin dakan na al’ummar kasar duk da matsin lamba da barazana daga makiya wadanda tun farkon yakin sukayi ta neman a tsagaita wuta.

An shafe kwana arba’in na yakin da Amurka da Isra’ila suka shelanta kan Iran.

Sanarwar ta majalisar koli ta ce ‘’ bisa umarnin jagoran juyin juya halin musulinci na kasar Ayatollah Seyyed Mojtaba Khamenei da kuma amincewar majalisar koli ta tsaron kasar, da kuma jajircewar Iran, da kuam ‘yan gwagwarmaya a fagen daga da kuma gazawar makiya na aiwatar da barazanar su, da kuma amincewa da sharuddan da Iran ta gabatar da kuma halatattun bukatun al’ummar kasar an amince da shiga tattaunawa da zata kai ga cimma yarjejeniya a cikin kwanaki 15 wacce zata tabbatar da yarjejeniyar da aka cimma ta hanyar siyasa.

Daga cikin sharudan da Iran ta gabatar ta hanyar Pakistan, za ta tafiyar da shige da fice a mashigar ruwa ta Hormuz, da kawo karshen yaki kan dukkan kungiyoyin gwagwarmaya, da janyewar dakarun Amurka a gabadayen sansanoninsu a yankin, biyan diyya ga Iran, dage gabadayen takunkumin da aka kakaba mata da kuma wasu kudurorin kwamitin gwamnoni da kwamitin tsaro na MDD da kuma mika mata kudadenta da aka rike a kasashen waje.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted