Canada, Japan , EU Suna Adawa da Kokirin Amurka Na Kashe ICC

Kasashen Canada da Japan Sun nuna rashin amincewarsu da takunkuman tattalin arzikin da gwamnatin Amurka ta dorawa kotun hukunta manya manyan laifuka ICC. Kamfanin dillancin

Kasashen Canada da Japan Sun nuna rashin amincewarsu da takunkuman tattalin arzikin da gwamnatin Amurka ta dorawa kotun hukunta manya manyan laifuka ICC.

Kamfanin dillancin labaran ISNA na kasar Iran ya nakalto wadan nan kasashe da kuma tarayyar  Turai suna fadar haka a birnin Roma na kasar Italia. Sun bayyana cewa akwai abun takaici wanda Amurka take yin a kokarin kakabawa kotun ICC saboda dakatar da ayyukanta.

Kasashen sun bayyana cewa suna goyon bayan matakan da kotun ta dauka don ci gaba da ayyukanta duk tare da barazanar da gwamnatin Amurka takewa kotun. Bayanin ya kara da cewa ‘ zamu ci gaba da hadin kai wajen kare koron kafin taron majalisar zartarwa ta kotun wanda za’a gudanar a cikin watan decemban shekara ta 2026 da muke ciki.

Shugaban kasar Amurka Donaltrump ya kakabawa kotun na ICC takunkumi jim kadan kafin a bawa shugaban Kotun kyautar Nobel wanda ya samarda yakin diblomasiyya tsakanin Amurka da Turai.

Nazhat Shameem Khan, mataikin shugaban kotun ya bayyana cewa takunkuman ba zasu dakatar da kotun daga gudanar da ayyukanta ba. Trump dai yana aikinwa HKI ce wacce kotun ta fadda sammacin kama Firimainitan kasar Benyamin Natan yahu da kuma Yauf Galanda tsahon ministen yakinsa saboda aikata kissan kiyashi a gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted