CAN: Yawan Yaran Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Ranar Jumma’a Sun Fi 300

A dai-dai lokacinda matsalolin tsaro suke kara tarbarbarewa a arewacin tarayyar Najeriya, kungiyar kiristoci ta kasa wato CAN ta bada sanarwan cewa yawan yaran da

A dai-dai lokacinda matsalolin tsaro suke kara tarbarbarewa a arewacin tarayyar Najeriya, kungiyar kiristoci ta kasa wato CAN ta bada sanarwan cewa yawan yaran da aka sace a ranar Jumma’an da ta gabat a makarantar St Mary a unguwar Papiri na karamar hukumar Agwara a jihar Naija ya kai 303. Daga cikin wadanda yan bingida suka sace har da malaman makarantar 12.

Jaridar Premiumtimes ta Najeriya ta nakalto shugaban kungiyar Can a jihar Bulus Yohanna yana cewa sun tabbatar  da wannan labarin ne a binciken da suka gudanar a makarantar.

Yohanna yace “Jimillar yan makaranta 303 ne aka sace, tare da malamansu 12, sannan wasu 88 da suka yi kokarin tserewa duk an kama su an tafi da su. Ya ce yan makarantar yara ne yan shekaru tsakanin tsakanin 10-18 ne.

Mr Yohanna ya musance sanarwan gwamnatin jihar kan cewa an sake bude makarantar bayan wannan al-amarin sata da kuma garkuwa da ya faru. Ya bukaci iyaye su kwantar da hankalinsu su kuma yi addu’a don dawowan yaransu cikin lafiya.

Matsalolin tsaro a cikin makon da ya gaba ta kadai ya kai ga yan ta’adda sun kai hare hare kan makarantu da dama a arewacin tarayyar Najeriya, wanda ya tilstawa gwamnatocin jihohi da dama rufe makarantu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments