CAF : Za a rika yin gasar AFCON duk bayan shekaru hudu, daga 2028

Hukumar kwallon kafa ta Afirka (CAF) ta sanar da cewa nan ba da jimawa ba za a rika gudanar da gasar cin kofin Afirka bayan

Hukumar kwallon kafa ta Afirka (CAF) ta sanar da cewa nan ba da jimawa ba za a rika gudanar da gasar cin kofin Afirka bayan shekaru hudu, maimakon bayan shekaru biyu.

Hukumar ta sanar da hakan ne, a Rabat, babban birnin kasar Morocco a jajibirin wasan farko na gasar cin kofin Afirka (AFCON).

Wannan babban sauyi ne ga gasar cin kofin Afirka, Tun bayan da aka fara buga ta a shekarar 1957 a Sudan, ana gudanar da gasar cin kofin nahiyar, duk bayan shekaru biyu.

A wani taron manema labarai a Rabat, Shugaban CAF Patrice Motsepe ya sanar da gabatar da gasar cin kofin Afirka bayan shekaru hudu, tun daga shekarar 2028, daidai da sauran manyan gasa kamar gasar cin kofin duniya da gasar cin kofin Turai.

Manufar gudanar da gasar cin kofin Afirka (AFCON) duk bayan shekaru hudu maimakon bayan shekaru biyu, wani abu ne da hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta bukata a baya.

A ranar Lahadi nan ne za’a bude gasar inda za’ayi wasan farko tsakanin Morocco mai masaukin baki da kuma Comoros.

Za’a kamala gasar a ranar 18 ga Janairu, 2026

Gasar, da aka tsara 2029 wacce za ta gudana a kasahen Kenya, Uganda, da Tanzania, yanzu za a gudanar da ita a shekarar 2028.

Bayan hakan, za a gudanar da gasannin AFCON na gaba a shekarar 2032, 2036, 2040, da sauransu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted