Burtaniya Ta Hana Makamai Zuwa HKI Har Sau 80

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Burtania ta bada sanarwan hana lasisin aika makamai har kunshi 80 zuwa HKI don ci gaba da kissan Falasdinawa a Gaza.

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Burtania ta bada sanarwan hana lasisin aika makamai har kunshi 80 zuwa HKI don ci gaba da kissan Falasdinawa a Gaza.

Kamfanin Parstoday ta nakalto IRNA na cewa, Stephen Doughly karamin ministan harkokin waje mai kula da yammacin Asia yana cewa, gwamnatin kasar Burtania ta sake hana wasu karin lasisin fitar da makamai zuwa HKI har guda 50 saboda kada ta yi amfani da su kan mutanen Gaza.

Labarin ya kara da cewa, kafin haka gwamnatin kasar Burtania ta hana lasisi har guda 30 na sayan makamai zuwa HKI saboda wannan dalilin. Majiyar ma’aikatar tsaron kasar ta Burtaniya ta bayyana cewa, duk tare da hana wadan nan makamai wucewa zuwa HKI amma an dage haramcin kan sassan jiragen yakin F-35 wadanda HKI take bukata don kula da irin wadannan jirage don ayyukan soje a Gaza dakuma kudancin kasar Lebanon.

Kasashen turai da dama sun bada sanarwan rage yawan makamai da tallafin da suke bawa HKI saboda ayyukanta da yankin yamma dakogin Jordan da kuma Gaza.  Sai dai wasu suna ganin wannan a zance ne kawai amma a aikace makamai suna kwarara daga kasashen Turai zuwa HKI wadanda take amfani da su a kan falasdinawa a duk yankunan kasar da ta mamaye.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted