Mohammad Elburada’I wanda ya karbi lambayar yabo ta nobel ta zaman lafiya kuma tsohon daraktan hukumar kula da makamashin ta duniya IAEA yayi gargadin cewa duk matakin kai harin soji da amurka zata dauka kan kasar iran zai zama na rashin hankali ne, kuma zai kara haifar da tashin hankali da barna ne, tare kuma da jawo mummunan asarar a yankin yammacin asiya
Yace ina kira ga dukkan wanda ke iya yin tasiri kan wannan mutumin yayi duk abin da ya kamata yayi amfani da karfinsa wajen hanashi kaddamar da wani yaki, wanda afili yana nufin shugaban kasar Amurka ne Donald Trump
Elburada’I ya karbi kyautar lambar yabo ta nobel ta zaman lafiya ne a shakara ta 2005 a kokarin da yayi a hukumar nukiliya ta duniya wajen hana karkarar da makashin nukiliya zuwa ayyukan soji, ta yi gargadi a lokuta da dama game da matakan da Amurka ke dauka na kara tsananta yanayin da ake ciki
Daga cikin gargadin da yayi daidai da furucin da yayi a baya, inda ya kwatanta yanayin da ake ciki yanzu da abubuwan da suka faru kafin mamayar da amurka ta jagoranta a kasar iraki a shekara ta 2003 yace yaki ne da ya sabawa doka da ma hakkin dan adam, wanda aka gina akan karya na kasancewar makaman kare dangi, kuma ya haifar da matsaloli masu yawa ga alummar yankin da ma zaman lafiya.