Bola Tinubu Zai Gabatar Da Daftarin Kasafin Kudin Shekara Ta 2026 Ga Majalisun Tarayya

 Majalisar Dattawa da ta Wakilai sun sanar da shirin karbar daftarin kasafin kuɗin shekarar 2026 a hukumance, yayin zaman hadin gwuiwa da aka shirya gudanarwa

 Majalisar Dattawa da ta Wakilai sun sanar da shirin karbar daftarin kasafin kuɗin shekarar 2026 a hukumance, yayin zaman hadin gwuiwa da aka shirya gudanarwa a yau Juma’a.

Sanarwar na kunshe ne a wata wasika da Kakakin Majalisar Wakilai, Abbas Tajudeen, ya karanta a zauren majalisar a ranar Alhamis, inda shi ma Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya karanta makamanciyarta a zauren Majalisar Dattawa.

 Shugaban kasa Bola Tinubu, zai gabatar da daftarin kasafin shekarar 2026 da misalin karfe 2 na ranar yau Juma’a, kuma ana sa ran zaman zai koma zauren Majalisar Wakilai da misalin ƙarfe 1:45 na rana.

A wani bangare kuma, Majalisar Dattawa ta karbi wasiku biyu daban-daban daga Shugaban kasa Tinubu, A wasikar farko, Shugaban kasa ya nemi Majalisar Dattawa ta tabbatar da nadin Injiniya Saidu Muhammad, a matsayin Babban Shugaban Hukumar Kula da Man Fetur ta kasa (NMDPRA),

A wasika ta biyu kuma, Shugaban ya nemi tabbatar da nadin Mista Oritsemanori Sewa Inyosa, a matsayin Babban Shugaban Hukumar Kula da bayar da lasisin dakon man fetur zuwa ƙasar nan (NUPRC), bisa sashe na 11(3) na Dokar PIA 2021,

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted