Birtaniya Ta yi Barazanar Korar Jami’an Diflomasiyar Isra’ila

kasar birtaniya ta yi barazanar korar jami'an diflomasiyar isra'ila guda 27 ko ta janye matakinta

kafafen yada labaran Isra’ila sun nakalto cewa kasar birtaniya ta gargadin gwamnatin isra’ila cewa zata kori jama’an diflomasoyarta guda 27 daga birnin London  tare da iyalansu har sai telaviv ta janye batun rufe babban ofishin jakadancinta dake gabashin  birnin qudus da isra’ila ta mamaye

Jakadan birtaniya Simon walters shi ne ya aike da wannan sakon ga jami’an isra’ila a wannan litinin, London tana shirin korar jami’an diplomasiyan israila guda 1 maimakon jami’anta guda 27 da za su rasa aikinsu idan aka rufe ofishin jakadancita sai dai ma’aikatar harkokin wajen birtaniya ta tace komai kan batun kuma bata musanta ba

minisatan harkokin wajen isra’ila Gideon Saar ya bada umarnin rufe ofishin jakadanci a ranar alhamis mai zuwa da kuma karbe dukkan takardun ma’aikatanta, ofishin jakadancin dake makwabtaka da shaikh jarrah, dake gudanar da ayyukan daban da ofishin jakadancin birtaniya dake telaviv dake kula daharkokin siyasa da sauran alamuran falasdinawa a gabashin birnin qudus dake gabar yammacin  kogin jodan da aka mamaye da kuma yankin gaza kuma wannan martani ne kan matakin da birtaniya ta dauka na hana shigo da kaya zuwa ga yahudawan yan share wuri zauna ta barauniyar hanya a watan da ya gabata

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted