Search
Close this search box.

Bincike: Durkushewar Kamfanoni Ta Kara Rashin Aikin Yi Tsakanin Matasa

Ficewa da durkushewar manya manyan kamfanonin Nijeriya dana kasashen waje saboda matsalar tattalin arziki da rashin yanayi mai aminci na gudanar da harkokin kasuwanci na

Ficewa da durkushewar manya manyan kamfanonin Nijeriya dana kasashen waje saboda matsalar tattalin arziki da rashin yanayi mai aminci na gudanar da harkokin kasuwanci na daga cikin dalilan da suka haifar da karuwar rashin aikin yi a tsakanmin matasan Nijeriya.

Kusan kashi 70 na al’umma Nijeriya matasa ne da ke a kasa da shekara 30, ana ganin wannan a matsayin wani mataki da za a iya amfani da shi wajen bunkasa tattalin arzikin kasa, amma kuma sai gashi lamarin ba haka yake a Nijeriya.

A ‘yan shekarun nan, bayanai sun nuna cewa, a kwai haske a has ashen tattalinh arzikin da aka yi wa Nijeriya amma kuma sai ga shi rashin aikin yi a tsakanin matasa yana ta kara ta’azzara saboda yadda manya da kananan kamfanoni ke fuskantar cikas saboda matsalar tattalin arziki a kasar.

Bincike ya kuma nuna cewa, matasa da dama da basu da aikin yi saboda kullewar da kamfanoni da suka yi wasu ma sun fice daga Nijeriya saboda da yawa daga cikin matasan kuma basu da wani aikin hannu da suka kware a kai.

Rashin aikin yi a tsakanikn matasa na da illa mai yawa ga rayuwar matasa yana kuma da babbar illa ga tattalin arziki da tsaron kasa.

Duk rahoton da ke nuna an samu raguwa na rashin aiki a yi tsakanin matasa zuwa kashi 33.3 a shekarar 2021 zuwa kashi 32.5 a shekarar 2023 amma har yanzu matasan da basu da aiki kuma basu da wani nau’in karatu ko kwarewa sai karuwa suke yi a fadin kasa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments