Biden Ya Amince Da Sayarwa “Isra’ila” Makamai Na Dala Miliyan 680

Jaridar “Financial Times” ta bayyana cewa Shugaban kasar Amurka Joe Biden ya amince da a sayar wa HKI da makaman da kudinsu ya kai Dala

Jaridar “Financial Times” ta bayyana cewa Shugaban kasar Amurka Joe Biden ya amince da a sayar wa HKI da makaman da kudinsu ya kai Dala miliyan 680.

Jaridar  da ake bugawa a Birtaniya ta kuma ce,jami’an Amurka sun sanar da majalisar Congress shirin gwamanti na bai wa Isra’ila makamin          “ Jdams” tare da wasu albarusai  da kuma bama-bamai masu yawa.

Jaridar ta “Financial Times” ta kuma kara da cewa; Ana bayyana wannan irin shirin na sayar da makamai ne gabanin ayi shi, domin kaucewa kin amincewar majalisar kasar ta Congress.

Wannan cinikin makaman dai yana zuwa ne a daidai lokacin da kasar ta ‘yan sahayoniya take cigaba da yi wa mutanen Gaza kisan kiyashi.

A cikin shekara daya na yaki, Amurkan ta bai wa HKI kowane irin makami da bama-bamai da ta yi amfani da su akan al’ummar Gaza da kuma Lebanon.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments