Gwamnatin Jamhuriyar Benin, ta fitar da sammacin kame dan fafatukar nan Kemi Seba da ya shahawa wajen kalubalantar siyasar faransa a kasashen Afrika.
Matakin dai an zuwa ne kasa da mako guda bayan yunkurin juyin mulki da aka yi wa Shugaba Patrice Talon, wanda ya girgizar kasar.
Kotun Jamhuriyar Benin ta bayar da sammacin kama, Kemi Seba da Sabi Sira Korogone, shugaban kungiyar ‘Yantar da Jama’a (MPL), bisa zargin goyan bayan ayyukan ta’addanci” da kuma “tunzura mutane su yi bore.”
Mutanen biyu za su iya fuskantar hukuncin daurin shekaru biyu zuwa biyar a gidan yari da kuma tarar miliyan goma na CFA, a cewar wata majiyar shari’a.
Shi dai Kemi Seba, ya fitar wani bidiyo a ranar 7 ga Disamba inda ya yi murna da yunkurin juyin mulkin da aka yi wa shugaba Patrice Talon.
A cikin bidiyon, dan fafutukar ya yi nuni da wani yunkuri na farko da za a iya maimaitawa idan shugaban kasar bai sake duba ayyukansa ba, wanda hakan ya haifar da fushi daga hukumomi.
A lokaci guda kuma, an kama Candide Azannaï, tsohon Ministan Tsaro kuma babban jigo a jam’iyyar adawa, a safiyar Juma’a a Cotonou.
An kama shi ne a hedikwatar jam’iyyarsa, inda ‘yan sandan shari’a ke yi masa tambayoyi.
A yanzu haka, ba a fayyace ainihin dalilan kama shi ba. Duk da haka, Azannaï ya nisanta kansa daga juyin mulkin da bai yi nasara ba na ranar 7 ga Disamba.