Sakin Fursunonin Falasdinawan yana a karkashin musayar fursunonin da aka yi a tsakaninsu da yahudawan Sahayoniya,inda aka tsara cewa za a saki yahudawa 3 sai kuma Falasdinawa 90.
Kungiyar Falasdinawa da take kula da fursunoni ta sanar da cewa an saki mata 69, da kuma kananan yara 21. &9 daga cikin wadanda aka saki din mazauna yankin yammacin kogin Jordan ne, sai wasu 14 daga birnin Kudus.
Tun da safiyar jiya Lahadi ne Falasdinawa su ka saki fursunonin Sahayoniya 3, sai dai HKI ta yi jinkirin sakin Fursunonin Falasdinawan kamar yadda aka tsara, sai bayan jinkiri na sa’o’i 7.
Said a safiyar yau Litinin ne dai fursunonin Falasdinawan su ka isa garuruwansu saboda jinkirin na ganganci da ‘yan sahayoniya su ka yi wajen sakinsu.
A gefe daya, a daidai lokacin da fursunonin da aka saki suke isa yammacin kogin Jordan, ‘yan sandan HKI sun kai hari a cikin gidajen wasu daga cikinsu.
Majiyar hukumar agaji ta Falasdinawa ta bayyana cewa, ma’aikatanta sun yi wa Falasdinawa biyu da su ka jikkata magani, bayan da ‘yan sandan sahayoniya su ka jikkata su a gairn Biyutina a yammacin Ramallah.
Sai dai duk da kokarin da ‘yan Sahayoniya su ka yi na hana Falasdinawa farin ciki, daruruwa sun fito kan tituna domin tarbar ‘yan’uwansu da aka saki.