Baqa’i: Araqchi Zai Dawo Iran Lokacin Da Aka Tsara

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Kasar Iran ya bayyana cewa: Ba a tsawaita zaman Abbas Araqchi a birnin New York ba Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Kasar

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Kasar Iran ya bayyana cewa: Ba a tsawaita zaman Abbas Araqchi a birnin New York ba

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Kasar Iran Isma’il Baqa’i ya bayyana cewa: Ba a tsawaita zaman Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araqchi a birnin New York na Amurka ba.

A cewar Kamfanin Dillancin Labaran Mehr, Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Baqa’i, yayin da yake amsa tambaya game da ko an tsawaita zaman ministan harkokin wajen Iran a birnin New York ne saboda tattaunawar kai tsaye tsakanin Iran da Amurka, ya ce: “A’a, babu batun tsawaita lokacin.”

Dangane da komawar ministan harkokin wajen zuwa birnin Tehran, kakakin ya fayyace cewa: Shirye-shiryen dawowar Araqchi za ta ci gaba bisa ga shirin da aka tsara a baya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted