Iran: Ana Ci Gaba Da Tattaunawa Da Masu Shiga Tsakani

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ya bayyana cewa: Suna ci gaba da tattaunawa da masu shiga tsakani domin ba wa diflomasiyya damar yin nasara Ministan

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ya bayyana cewa: Suna ci gaba da tattaunawa da masu shiga tsakani domin ba wa diflomasiyya damar yin nasara

Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Abbas Araqchi ya tabbatar da cewa: Iran za ta ci gaba da bai wa diflomasiyya damar yin nasara ta hanyar ci gaba da tuntuɓar masu shiga tsakani.

A cewar kamfanin dillancin labaran Mehr na kasar Iran Abbas Araqchi ya rubuta a shafukan sada zumunta cewa: “Yayin da dakarun Iran jarumai suka shirya tsaf don kare ƙasarsu, Iran ta ci gaba da bai wa diflomasiyya damar yin nasara.”

Ya ƙara da cewa: “Suna ci gaba da tuntuɓar masu shiga tsakani don tattauna ra’ayoyin da za su tabbatar da aiwatar da shirin Iran na kwanaki bakwai cikin ƙasa da mako guda.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted