Bangaladesh Ta Kasa Samun Kudaden Kula da Yan Gudun Hijiran Rohinga

Shugaban rikon kwarya na kasar Bangladesh Muhammad Yunus ya bayyana cewa kasarsa ta kasa samun kudade daga cikin kasar don kula da yan gudun hijira

Shugaban rikon kwarya na kasar Bangladesh Muhammad Yunus ya bayyana cewa kasarsa ta kasa samun kudade daga cikin kasar don kula da yan gudun hijira na Rohinga wadanda yawansu ya kai miliyon 1.3.

Shafin yanar gizo na Labarai ArabNews na kasar Saudiya ya nakalto Yunus yana fadar haka a wani taron da aka gudunar a yankin Cox’s Bazar a bakin tekun Bagladesh dake kudu maso yabbacin kasar.

Labarin ya kara da cewa, kasar Bangladesh tana fama da matsalolin tattalin arziki da dama, wadanda suka sa ba zata iya daukar nauyin kula da wadan nan yan gudun hijira wadanda suke samun mafaka a wurare 33 a laradin na Cox’s Bazar.  Ya kuma kara da cewa, zai sake nanata wannan bukatar ga MDD a cikin watan satumba mai zuwa, da kuma kasashen duniya gaba daya. Ya ce a cikin kasafin kudin da suka lissafa na shekara ta 2025-26 ana bukatar dalar  Amurka miliyon $935, amma zuwa yanzu kasha 36% ne kawai aka samar da shi a cikin gida.

Yunus ya kara da cewa wadannan yan gudun hijira suna bukatar taimako, har zuwa lokacinda zasu koma gida. Tun shekara 2021 ne sojoji suka yi juyin mulki a kasar Myanmar, inda sojojin suka faran korar yan Kabilar Rohinga musulmi da suke kasar, kuma dukkan kokari na sasantawa tsakanin gwamnatin sojojin na Myanmara da yan tawayen Arakan na Rohinga bai kai ga nasara ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments