Aljeriya ta kori sama da mutane 30,000 zuwa Nijar a shekarar 2024, a cewar wata kungiya mai zaman kanta ta Alarme Phone Sahara.
A cikin rahotonta na shekara-shekara, Alarme Phone Sahara ta ce wannan adadi ya zarce duk wanda kungiyoyi masu zaman kansu suka fitar a shekarun baya.
A 2023, fiye da 26,000 Aljeriya ta kora, wanda kuma kungiyar ta yi tir da yanayin da ake korar tasu.
A cewarta, ana iya watsi da bakin hauren a tsakiyar hamada, a kan iyakar kasashen biyu, inda daga nan ne za su yi tafiya mai nisan kilomita da yawa don isa garin Assamaka da ke iyaka da Nijar, inda wasu ke isa wurin cikin rashin lafiya.
APS ta kuma yi Allah wadai da kame-kamen da jami’an tsaron kasar Aljeriya ke yi, da farmakin da suke kaiwa bakin hauren.