Baka’i: Ba Za A Iya  Bayyana Laifukan HKI Da Kalamai Ba

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen JHM ta bayyana cewa; Ba zan iya samun kalmomin siffata laifukan da HKI take tafkawa a Gaza ba. Dr. Isma’ila Baka’i

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen JHM ta bayyana cewa; Ba zan iya samun kalmomin siffata laifukan da HKI take tafkawa a Gaza ba.

Dr. Isma’ila Baka’i wanda ya gabatar da taron manema labaru na mako-mako ya ce; A cikin shekaru biyu na bayan nan mun ga yadda ‘yan sahayoniya suke yin kisan kiyashi da Gaza, sannan kuma su ka dora da amfani da yaunwa a matsayin makamin kisa.

Haka nan kuma Dr. Baka’i ya ce; An shiga kwanaki 140 yankin Gaza a killace, kuma a cikin wadannan kwanaki biyu zuwa uku mun ga yadda Falasdinawa suke kara shiga cikin wahala, amma kuma an hana shigar da kayan abinci zuwa yankin Gaza.

Dr. Baka’i ya ce; Abin takaici ne cewa lamirin jinsin bil’adama a wannan lokacin yana cikin maye,muna ganin yadda ake kulla kawance da kasar da ba ta da wani aiki sai laifuka da kisan kiyashi, su kuma kungiyoyin kasa da kasa sun kasa yin komai.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci Ta Iran din ya kuma yi ishara da yadda a cikin sa’oi 24 da su ka gabata aka yi wa mutanen Gaza 15o kisan kiyashi.

A dalilin hakan, Baka’i ya ce, babu wata kalma da za ta iya bayyana hakikanin abubuwan da suke faruwa na laifuka masu yawa.”

Haka nan kuma ya yi kira ga kasashen wannan yankin da su yi aiki da nauyin da ya rataya a wuyansu.

Dangane da abinda kungiyar kasashen musulmi za ta iya yi, kakakin ma’aikatar harkokin wajen na Iran ya ce, da akwai bukatar ayi taron gaggawa domin tattauna wannan batun, kuma tuni Iran ta mika bukatar yin haka ga cibiyar kungiyar ta kasashen musulmi.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments